Yan kungiyar Boko Haram Sun Kai Hari Cibiyar Kiwon Lafiya A Jihar Yobe .

boko-haram
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Wasu da ake zargi yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari cibiyar kiwon lafiya inda suka kwashe magunguna a Gumsu dake kan iyaka da yankin jihar Yobe.

Yan ta’addan da suka fito daga dajin Sasawa kusa da Bayamari akan titin Geidam sun kwace motar ambulace kafin su kai hari cibiyar da misalin karfe goma na dare.

Yayin tattabar da lamarin jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda mataimakin supritandan yan sanda Dungus Abdulkarim ya bayyana cewa yan ta’addan sun fara harbe harbe domin su tsoratar da jama’a da jami’an yan sanda.

Sun kwace motar ambulance cike da magunguna hakan ya sanya mazauna yankin tserewa zuwa daji.

Wani mazaunin yankin Audu Hussein yace suna cikin fargaba da tsoro, haka wani mazaunin garin mai suna Audu shima ya bayyanawa manema labarai cewa sun dade suna cikin fargaba tun kafin yan ta’addan su shigo cikin karin amma sun godewa Allah da ya sanya babu wanda aka kasha a harin.

Yace sun dade suna samun labarin an gay an ta’addan a nesa da garin Gumsa kafin su kawo harin nan, kuma abin da mamaki ace sun shigo garin kuma suka dauke mota cike da magunguna cikin sauki.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply