Yan Kungiyar Boko Haram Sun Kafa Tutarsu A Geidam Dake Jihar Yobe.

Yan kungiyar Boko Haram sun kafa tutarsu a wasu sassa na yankin garin Geidam dake jihar Yobe.

Hakan yazo bayan kwana 2 da yan kungiyar suka kai hari karamar hukumar ta Geidam dake jihar.

Garin Geidam dai shine garin sabon mukaddashin ‘yansanda na kasa malam
Usman Alkali Baba.

Wasu daga cikin mazauna garin sun bayyanawa gidan talabijin na Channels cewa yan kungiyar ta Boko Haram sun kafa tutocinsu a wasu sassa na garin inda suka dinga bi gida-gida suna yiwa mutane wa’azi kan akidarsu.

Duk da har yanzu akwai jami’an sojin a Geidam har yanzu ‘yan kungiyar na yankin kuma bai hana su cimma burinsu ba.

Haka nan sun lalata wasu kafofin sadarwa na garin kuma an saka iyalai da dama cikin damuwa na rashin hira da yanuwansu.