Yan Kungiyar Asiri Sun Cire Al’auran Wata Yarinya Akan Naira Dubu Dari 5 A Jihar Bauchi.

Nigerian-police-thumb
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

An kama wasu mutane 2 yan kungiyar asiri da ake zargin su da cire al’auran wata yarinya karama a jihar Bauchi kan naira dubu dari 5.

Wadanda ake zargin Abdulkadir Wada da Adamu Abdulrauf sun bayyana cewa wani matsafi ne ya nemi da su kawo al’auran yarinya mace wanda yayi alkawarin zai basu wannan kudi.

Wadanda ake zargin sun fito ne daga karamar hukumar Jama’are wanda jami’an yan sandan jihar suka kama su.

Yayin da suke bayyana yadda abin ya faru, sun bayyana cewa sun je Kwata inda yayan yarinyar yake da zama, inda suka kama yarinyar zuwa wani ginin da ba a kammala shi ba kuma suka kashe ta.

Ana shine bangaren kuma Abdulrauf ya bayyana cewa bai kashe ta ba inda yace Abdulkadir ne ya kashe ta yayin da ya same shi a gida kuma yake bayyana masa cewa sun je wajen matsafi shi da abokin shi wanda yace su aikata haka kafin su samu naira dubu dari 5 da yayi musu alkawari.

Mai Magana da yawun rundunar yan sandan jihar Bauchi DSP Ahmed Muhammad Wakil ya bayyana wa manema labarai cewa za a tura wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar sun kamala bincike.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply