Yan Kasuwar Kasar Ghana Sunyi Barazanar Kaiwa Takwarorinsu Na Najeriya Hari

Yan kasuwar kasar Ghana sun roki kwamitin kungiyar ‘yan kasuwar da ya cigaba da aikinsa na rufe shagunan baki masu saida kaya a kasar tasu wadan da basu da takar dun shaida.

hakan ya biyo bayan shirin da ‘yankasuwar na Najeriya ke yi mazauna kasar Gana don kinamincewa da abubuwan da kasar Ghana ke musu bayan yarjejeniyar dake tsakanin kasashen biyu a rahoton da Ghanaian Times ta fitar .

San nan rahoton na Ghanaian Times yace dabi’un da yan kasuwar ta Najeriyar suke yi a kasar tasu cin mutunci ne wanda hakan yake harzuka hukumomin na da mutanen na Ghana.

Haka nan ‘yan kasuwar na Ghana sun umarci kwamiti kan kasuwannin da ya yi gaggawar cigaba da ayyukans aba tare da bata lokaci ban a rufe shagunan yan Najeriyar donhakan na harzuka yan kasar ta Ghana a kasuwanni.

Nkem Tony Onyeagolu, tsohon shugaban yan Najeriya dake yankin Ashanti ya roki Shugaban kasar Ghana, Nana Addo Akufo-Addo da ya bada umarnin sake bude shagunan yan Naeriya da aka rufe.

Onyeagolu yace tun da aka rufe musu Shaguna abubuwa sun yiwa mutanensu ‘yan kabilar Igbo zafi.

ya kuma bayyana cewa yawancin su abun ya sa sun shiga wasu hali, wasu na cikin bashin da sun ka biya.

A nashi bangaren shugaban kungiyar ‘yan kasuwar na Najeriya Chukwuemeka Nnaji yayi kira ga shugaban na Ghana Akufo-Addo, shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, kungiyar kasashenyammacin Afrika ta ECOWAS dasu shiga wan nan lamarin kuma su sa a dena kaiwa muatnensu hari kamar yadda akayi alkawari a sakon da aka fitar.