
Kasuwan dabbobi na garin Maiduguri daya kasance mai yawan dabbobi a yankin Afrika ta yamma a yanzu harkoki ya koma baya sakamakon rikicin yan ta’addan BH na tsawon lokaci da ya gurgunta kasuwancin.
Kusan dukkan masu harkar dabbobi a kasuwannin a yankin tabkin chadi sun dakata sakamakon tasirin ta’addanci a bangaren.
Wani mai kasuwancin dabbobi Mal. Baba Gana yace a baya ana kawo dabbobi da suka hada da awakai, tumakai, da dawakai daga kasuwannin ciki da wajen kasar nan kafin barkewar rikicin yan ta’addan Boko Haram .

Wani mai sana’ar dake zama a Muna Kumburi yace ya sayar da dukkan dabbobin sa inda ya koma Maiduguri da zama.
Yanayin tsaron da ake fama da shi a Maiduguri yana dad a karuwa wanda yake goge tsammanin karshen rikicin, sannan titin Maiduguri zuwa Kano da a baya yafi kowani titi samun tsaro a yanzu ya zama hanyar kawo hari da kuma sace jama’a.
wanda a kwanan nan aka sace mutane 35 a hanyar Auno zuwa Jakana wanda ya sanya gwamna Zulum cewa sakacin jami’an sojoji
Gwamnan ya bayyana kaduwa matuka yayin day a ziyarci wurin ya kuma nuna damuwa matuka da faruwar hakan.
