Yan Jaridu Mata Sun Yi Kira Ga Sabbin Hafsoshin Sojoji Da Su Kara Kaime A Yaki Da Yan Boko Haram

NUJ
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar mata yan jaridu ta kasa tayi kira ga sabbin hafsoshin sojoji da su dawo da sabbin dabaru domin fuskantar kalubalen tsaro da ya zama barazana ga zaman lafiyar a kasa.

Sanarwar wanda shugaban kungiyar Ladi Bala ta sanaywa hannu, ta yabawa shugaba Buhari kan nadin sabbin hafsoshin da yayi domin inganta yaki da yan ta’adda.

Sanarwar ta kara dacewa dukkan cibiyoyin rashin tsaro da ta addabi kasar nan yafi shafar mata, inda tace babu wani kasa da zata cigaba yayin da al’ummar ta mafi yawa matane da yara kuma suna cikin barazana.

Daga karshe sanarwar ta kara dacewa akwai bukatar gwamnatin tarayya ta samar da dukkan abubuwan bukata na yaki ga jami’ai da kuma jin dadin su domin yaki da yan kungiyar Boko Haram, fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply