Yan Gudun Hijira Borno Dake Kasar Kamaru Sun Sa Ranar 27th Na Watan Nan Domin Dawowa Najeriya

images (19)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Yan gudun hijira yan borno dake kasar kamaru sun sa ranar 27th na watan nan domin dawowa Najeriya bayan ziyarar da gwamna Zulum ya kai musu.

Biyo bayan ziyarar kwanaki biyu da gwamnan jihar borno prof. babagana umara Zulum, an samu matsaya tsakaninsa da hukumomin kamaru domin fara jigilan dawoda yan gudun hijiran najeriya zuwa jihar borno da yardan su wanda zai soma aiki 27th na wannan watan da muke ciki, sannan za’a cigaba da aikin 7th ga watan mayu na wannan shekarar.

Kusan mutane 46,000 yan Najeriya, yawanci daga jihar borno ne ke zaune a sansanin yan gudan hijira dake Minawao a Mokolo, a arewacin kamaru.

Gwamna Zulum tareda ma’aikatun hukumar agajin gaggawa ta kasa dana kamaru, sunje sansanin na miawao ranar laraba kafin komawar su birnin Maroua dake arewacin kamaru.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply