Yan fansho A Jihar Bauchi Sun Koka Akan Gwamnatin jihar ta Biyasu Harkokin Sa.

pensioners-300x225
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar yan fansho ta Najeriya, reshen jihar Bauchi, ta roki gwamnatin jihar da ta biya bashin da yan fansho da wasu mambobinta ke binta na watanni goma sha daya.

Kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa ‘yan fansho sun shiga cikin matsalar albashin a jihar da kuma jerin sunayen’ yan fansho da ma’aikatan gwamnati.

Shugaban kungiyar Malam Aliyu Dogoro ya yi wannan rokon ne a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Bauchi ranar Jumaa.
Ya ce rashin biyan hakkokin yan fansho da gomnati keyi na jefa su, cikin mayuyacin hali

Dogoro ya ce wasu daga cikinsu suna fama da cututtukan da suka shafi shekaru kamar ciwon sukari da hawan jini, da sauransu.
Shugaban ya yi alkawarin cigaba da matsa lamba domin jin dadin mambobin nasa.
A halin da ake ciki, Alhaji Mukhtar Gidado, babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga Gwamna Bala Mohammed, ya ce gwamnati na yin duk abin da ya dace domin fara biyan hakkokin yan fansho.
Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan 27 a cikin kasafin kudi na 2021 domin biyan hakkokin giratuti na maaikatan da suka yi ritaya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply