Yan Boko Haram Sun Kashe Yan Sanda 4 A Jihar Yobe.

boko-haram-group-writes-european-union-over-conduct-of-french-countries-around-lake-chad
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Yan kungiyar Boko Haram sun kashe yan sanda 4 da mazauna garin Bayamari 7 dake jihar Yobe.

Yayin tabbatar da lamarin da ya faru ranar Laraba wani jami’in sa kai na CJTF dake aiki da sojoji wajen yaki da yan ta’adda Audu Yahaya ya bayyana cewa an kashe mazauna garin 7 da yan sanda 4 yayin da suke kokarin kare al’umma daga fadawa cikin harin.

Yace bayan yan ta’addan sun tsere daga jami’an sojoji, sun gudanar da harin a kauyen Bayamari da misalign karfe 12 da minti 15 na rana.

Yace yan sandan sun rasa rayukan su yayin kare al’umma daga harin yan ta’addan.

Yace yan ta’addan sun gudanar da harin su ne daga sabon sansanin su dake dajin Malari Zango, Abduri da kuma Buhari.

Sauran mabuyar su sun hada da Degltura, Kayidiri, Garin Liman, Gumsari Gagala da Gorrgo a karamar hukumar Yunusari.

Ya kara dacewa a kwanan nan yan ta’addan Boko Haram sun tsere daga kananan hukumomin Bama, Gwoza da Damboa da kuma yankin tabkin chadi inda jami’an sojoji ke gudanar da aiki.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply