Yan Boko haram Sukai Hari A Kauyan Wamdeo A Jihar Borno

boko-haram
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

A kalla sama da gidaje talatin tare da kayakin amfanin gona ne yan kungiyar Boko haram suka tarwatsa a kauyen Wamdeo dake karamar hukumar Askira/Uba cikin jihar a daren talata.

Maharan sunshigo garin ne da misalin karfe shida da rabi na yamma inda suka dauki awwanni biyu sunayi.
Wani mazaunnin garin ya bayyana wa gidan radiyo Dandal Kura Radio International bacin ransa a game da barnnan da yan kungiyar sukayi.

Wajajen da suka tarwatsa sun hada da shaguna dake cikin kasuwa,gidaje,da kuma gidajen bauta.

Gidan radiyo Dandal Kura Radio International ta kara da cewa jama’ar garin sunyi gudun tsira zuwa dazuka dake kusa da kauyen nasu.

Wani jami’in soji wanda aka sakaya sunnan shi yace sun kashe wasu yan kungiyar a kauyen chul bayan sun baro kauyen wandiyo.Yace anyi amfani da jiragen yaki ne wajen tarwatsa wasu daga cikin yan ta’adan.
COV/PLP/BBW BBW

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply