Yan Bindiga Sun Kashe Matafiya 16 A Kan Hanyar Abuja Zuwa Kaduna.

Terrorists-Kill-26-In-Katsina-Community-As-Buratai-Tours-The-State
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

A kalla matafiya 16 ne yan bindiga suka kasha a babban hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Kamar yadda rahotanni ya nuna daga fadar gwamnatin jihar Kano, matafiyan sun taso ne daga jihar Kano domin kasuwanci.

Rahotanni ya bayyana cewa yan kasuwa maza da mata sun kasance daga karamar hukumar Danbatta ne na jihar Kano.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana kaduwar sa matuka bisa kisan da akayiwa yan kasuwan kamar yadda babban sakataren yada labarai Abba Anwar ya fitar.

Yace ya kadu matuka bisa kisan da akayiwa yan asalin jihar Kano akan titin Abuja zuwa Kaduna, ya mika ta’aziyar sa ga iyalan wadanda abin ya shafa da al’ummar karamar hukumar Danbatta da na jihar Kano baki daya.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply