Yan Bindiga Sun Kai Hari Kasuwar Dabbobi A Kasar Burkina Faso

BURKINAFASO
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin kasar Burkina Faso tace yan bindiga sun kai hari kasuwar dabbobi da kuma kan motocin masu bada agaji inda suka kashe mutane 25.

Mutane da dama sun samu raunuka a harin da aka kai kasuwar dake gabashin kauyen Kompienga, haka nan an kashe fararen hula 5 da sojoji 5 a arewacin kauyen Foube.

An bayyana cewa motocin masu bada agajin na dawowa daga Foube ne bayan sun kai kayayyaki. Wasu sassa na kasar Burkina Faso na fama day an bindiga dake da alaka da al-Qaeda, ISIL da ISIS tun shekarar 2017.

An kashe daruruwan mutane a shekarar da ta gabata a yankin Sahel inda fiye da mutane rabin miliyan ne suka tsere daga gidajensu, har ya jawo rikicin addini da kabilanci.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply