WHO Ta Bayyana Cewa Najeriya Bata Cikin Kasashe Masu Polio A Yanzu

wHO-small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

kungiyar lafiya ta duniya ta bayyana Najeriya a matsayin kasar da bata dauke da cutar polio, bayan da ta gama bincikenta.

kungiyar ta majalisar dinkin duniya ta bayyana hakan ta bakin ofishinta dake Afirika na garin Brazzaville dake kasar Congo,a shafinta na twitter.

Inda tace a yanzu Najeriya ta kammala matakan da ya kamata na tsallake cutar Polio wadda sashin hukmar na Afrika ya tabbatar babu cutar a kasar.

Dr Faisal Shuaib babban Darakta na kiwon lafiya matakin farko ne ya bayyana hakan a shafinsa na twitter inda ya bayyana cewa ya zama tarihi.

Najeriya ta samu ta cimma wan nan sakamakon kokarin shugaban kasar Muhammadu Buhari da kuma taimakon Aliko Dangote da Bill Gates.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply