WhatsApp ta kusa fara gudanar da ayyukansu a’urori daban daban ba tare da layin yanar gizo ba

Nan bada daewa ba WhatsApp zai kasance a kan na’urori da yawa ba tare da jona intanet ba.

Ance ana sa ran WhatsApp zai fara aikin a cikin watanni 2 masu zuwa ga duka masu gwajin Android, iOS beta.
Siffar, da ake kira Multi-device, a halin yanzu tana kan ci gaba.

Da zarar an ƙaddamar dasu, masu amfani zasu iya haɗa abubuwa har zuwa na’urori huɗu zuwa asusun su na WhatsApp.

Tashar sakonnin rubutu da bidiyo ta WhatsApp ta sanar da cewa nan ba da dadewa ba za ta kaddamar da wani sabon fasali wanda zai ba masu amfani damar amfani da aikace-aikacen a kan na’urori da yawa ba tare da sun samu intanet ba.

A cewar WABetaInfo, ana amfani da fasalin na’urorin masu yawa a halin yanzu amma ana sa ran farawa a cikin watanni biyu masu zuwa ga masu gwajin Android da iOS beta.

Mark Zuckerberg da Will Cathcart sun tabbatar da cewa na’urori masu yawa suna nan zuwa cikin watanni biyu.

Da zarar an fara amfani da su, masu amfani da shafin za su iya hada abubuwa har zuwa na’ura hudu zuwa asusunsu na WhatsApp, in ji Will Cathcart, in inda ya kara da cewa WhatsApp din zai bai wa masu amfani da damar yin hijrar daga bayanansu tsakanin na’urorin iOS da Android.

Shafin yanar gizon ya kara bayyana cewa kiran murya da bidiyo zasuyi aiki a dukkannin na’urorin da aka alakanta, sannan ya kara da cewa wadanda basu yi wani abu ba ta WhatsApp dinsu ba zasu iya karbar kira ko sakonni baWhatsApp.