Wata Kotu A Jihar Borno Ta Yankewa CJTF Hukuncin Shekaru 10 A Gidan Yari.

borno-state-small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Wani babban kotu dake zaman ta a Maiduguri ta yankewa wani jami’in sa kai na CJTF mai suna Kwaji Yakubu hukuncin shekaru 10 a gidan yari bisa zargin kisan kai kamar yadda sashi na 224 na dokar jihar nan ta shimfida.

Mai shari’a Alkali Gana Wakil na babban kotu mai number 11dake Gidan Madara ya bayyana cewa an kama mai laifin ne wajen amfani da bindiga wanda yayi sanadiyar mutuwar Muhammad Ibrahim dake unguwar Bulumkutu.

A wata sanarwa, mai laifin ya bayyanawa yan sanda cewa bindigar ta fashe ne ba tare da yasan hakan zai faru ba.
Kotu bata amince da abinda ya fadawa yan sandan ba in da tace bindiga bata fashe b aba tare da an taba ta ba.

Mai shari’a Alkali Gana yayi kira ga shuwagabanni da cewa kada bu bari maharba su rike bindiga a gidajen su ko wuraren taron jama’a.

Daga karshe mai shari’an ya umurci yan sandan da su rike bindigar kuma yace su cigaba da kula da harkokin ire iren jami’an sa kai na CJTF musamman wajen daukar bindigogi zuwa gidajen su.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply