Wata Gidauniya Tabada Gudumawar Motocin Asibiti Guda 3 Da Takunkumin Fuska Dubu 50 Ga Gwamnatin Jihar Bauchi

map-of-bauchi-state
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Wata gidauniya a ranar litinin tabada gudumawar motocin asibiti guda 3 da takunkumin fuska dubu 50 ga gwamnatin jihar Baushi a matsayin gudamwarta na yakar annobar covid 19 a jihar.

Yayin dayake gabatar da kayayyakin ga gwamnatin jihar a gidan gwamnatin jihar Bauchi.
shugaban gidauniyar Alhaji Abdussamad Isyaka Rabiu yace sunyi gudumawar ne musamman don su marawa wa gwamnati baya cikin yakar cutar da takeyi.

Isyaka Rabiu ya yaba da irin ayyuka da gwamnan Bala Abdulkadir Mohammed yayi a yakar cutar kuma yace gidauniyar zata bada goyon bayanta a ko da yaushe domin cimma bukatun da ake nema.

Dr Aliyu Idi Hong tsohon ministan lafiya daya wakilci shugaban ya godewa gwamnatin jihar bisa amincewa da aiki tare da gidauniyar.

Anasa bangare , gwamna Bala Mohammed ya mika kayayyakin ga kwamtin karta kwana na yaki da cutar Covid 19 na jihar.

kuma yayi umarni da a rabasu yadda ya dace.

Ya kuma ce gwamnatun sa ta shirya abota da gidauniyar sannan ya godewa mambobin na CACOVID-19 da irin abin azo a gani da sukayi cikin yaki da annobar a najeriya

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply