
Wata gidauniya na Milestone Rehabilitation tare da tallafin kungiyar nahiyar afirka African Transitional Justice Legacy Fund sun taimaki wata yar jihar Borno mai suna Aisha yar shekaru 14 da yan kungiyar Boko Haram suka sace kuma suka ci zarafin ta.
Ta kasance cikin daruruwan mata a jihar Borno wadanda suka fuskanci cin zarafin jinsi wanda suka tilsta mata aure sannanta kubuta da jariri dan wata bakawai.
Gidauniyar ya kasance mai bada tallafi ga kungiyoyin da suke yankunan da suka fuskanci tashin hankali da kuma, kare hakkoki gaskiya da kuma sulhu.

A karkashin abota tsakanin kungiyoyin 2, gidauniyar Milestone Rehabilitation ta samar da kafa domin taimakawa mata da suka fuskancin cin zarafi sanadiyyar ta’addancin Boko Haram, da kuma mu’amala da juna domin samun maslaha.
