
Wasu ‘yan gudun hijirar da ke tafiya a kan hanyar Dikwa – Ngala sun mutu ta hanyar wani bam da aka dasa, a cewar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno SEMA.
A cewar daraktan ayyuka na hukumar, Abdullahi Suleiman, yace lamarin ya faru ne da safiyar Laraba da misalin karfe 11:00 na safe.
Ya bayyana cewa ‘yan gudun hijirar suna kan hanyar kasuwanci ne a kan hanyar Dikwa – Ngala a lokacin da wani abin fashewa ta fashe da su a ƙauyen Moula, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane uku.

Bugu da ƙari kuma, ya ce wasu takwas sun ji rauni kuma a yanzu suna karɓar magani a asibitin Fhi360 da ke Dikwa.
