Wasu mutane sun tsere daga gidajen su sakamakon hari da yan kungiyar Boko Haram suke kaiwa a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

boko-haram
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Yawancin mazauna kauyukar dake kan titin Maiduguri zuwa Damaturu sun tsere daga gidajen su sakamakon wayar gari da hare haren yan kungiyar Boko Haram.

Tashin hankali ya tsananta a karshen makon daya gabata sakamakon rashin tsaro a garin Auno da kewayensa dake cikin yankin a karamar hukumar Konduga.

Yan tada kayar baya sun addabi masu motoci da mazauna kauyukan dake yankin na tsawon makonni duk kuwa da cewa akwai shingaye na sojoji dake duba ababen hawa a titin.

Mazauna kauyen sun koka cewa a kullum ana kashe wasu daban tare da sace wasu masu yawa.

Wani mazaunin garin Auno, Bukar Auno ya tatauna da komandan rundunar sojoji inda yace basa bukatar wani shinge a tsakiyan garin.

Ankafa shingen ne kimanin wata guda daya shude inda yace basu san manufar kafashi a cikin garin ba maimakon a wajen garin ba.

Ya roki gwamnatin jihar Borno datasamawa yan sintiri da maharba da makaman da suke bukata don yaki da yan ta’adda yana mai cewa kashi 75 cikin 100 na jama’ar garin duk sun gudu.

Shugaban kungiyar kare hakkin jama’a ta Network of civil society dake jihar Borno Ahmed Shehu ya tabbatar da cewa jama’ar garin na Auno sun tsere zuwa Maiduguri.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Related stories

Leave a Reply