
Wasu masu bincike sun bukaci kara farashin sigari a Najeriya da kashi 50 domin rage mutuwar mutane sama da dubu 23 su mutu sai kuma mutane sama da dubu dari 6 sun raunana kuma sun kamu da cututtuka.
Masu ruwa da tsaki a wajen taro kan kasuwancin tabar a Najeriya wanda aka gudanar a jami’ar Ibadan sun bada nasu jawabin
Kanfanin dillancin labaran Najeriya ta rawaito cewa cibiyar bincike na tattalin arziki a Afrika ne suka shirya taron.
Babban mai bincike na cibiyar Dr Adedeji Adeniran yayi kira ga gwamnati da ta maida hankali kan kasuwancin ta domin rage matsalolin ta.

A nashi bangaren Dr Iraoya Augustine yace kasuwancin tabar yayi yawa a Najeriya inda ya bukaci da a kara haraji wanda yace hakan shi zai rage, ya kara dacewa yawan mace mace, yawan cutar daji da sauran cututtuka zai ragu idan aka kara haraji da kashi 25.
