Wasu daga cikin yanmatan makarantar Chibok sun dawo gida a jiya

chibokgirlsthumb
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Da dama daga cikin yan matan Chibok da aka sace daga makarantar sakandire ta yan mata dake garin Chibok dake jihar Borno sun tsere daga hannun wadanda sukayi garkuwa dasu.

Wakilinmu ya hada mana rahoto cewa an gano yan matan sun gudu a jiya bayan wasu hare-hare da aka kaiwa yan kungiyar a maboyar ta Boko Haram dake dajin Sambisa.

Mazauna garin na Chibok sun nuna murnarsu yayin da suka samu rahoton dawowar yan matan da aka sace tun shekarar 2014 sun dawo gida.

Wani mahaifi mai suna Malam Madu Mutta ya bayyana wa manema labarai a Maiduguri cewa karamar hukumar ta Chibok ta cika da murna yayin jin labarain.

Wata majiyar ta bayyana cewa cikin wadanda suka tsiran sun hada da Halima Ali wadda akace ta auri wani kwamanda na kungiyar ta Boko Haram.

Haka nan sakataren kungiyar iyaye da malaman makarantar ta Chibok Lawal Zannah yace tabbas wasu daga cikin yaran sun tsira amma bai san yawansu ba.

Haka nan gwamnatin jihar tace taji labaran amma har yanzu bata tantance sahihancin labarin ba.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply