Wani Soja Ya Bude Wuta Akan Wasu fararen hula a Maiduguri .

armytroopswide
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Wani soja ya bude wuta ga fararen hula a wani wajen shakatawa na sojojin da basa aiki a nan Maiduguri.

Wakilin mu ya rawaito mana cewa jami’ai sun tafi da sojan tare da abokan wadanda abin ya shafa, lamarin da ya faru da misalign karfe 8 na dare yayi sanadiyar mutuwar mutane 3 sannan wasu 3 sun samu rauni.

Wata majiya ta sanar da gidan radiyo Dandal Kura cewa Barka da Zuwa dake kusa da titin tashan Baga, ya kasance wajen taron bata gari da sojojin da aka kore su a aiki.

Idan za a iya tunawa dai gwamnatin jihar Borno a shekarar 2018 ta bada damar rushe irin wuraren nan da ta kira da mahadar shaye shaye su 47.

Bayan rushewar ne gwamantin jihar ta gina asibiti mai gadaje 50 a unguwar Bolori na biyu domin inganta kiwon lafiya a yankin.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply