Wani Dan Najeriya Mai Shekaru 27 Suleiman Isa Ya Auri Masoyiyar Sa Jennie Sanchez Yar Kasar Amurka

FB_IMG_1607876484388
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Wani dan najeriya mai shekaru 27 Suleiman Isa ya auri masoyiyar sa Jennie Sanchez yar kasar Amurka mai shekaru 46 da suka hadu ta instagar.

Kamfanin dillancin labaran najeriya NAN ta ruwaito cewa daruruwan yanuwan da abokan arziki ne suka halarci bikin da aka daura masallacin Jumma’a na Panshekara dake karamar hukumar Kumbotso na jihar Kano.

Angon Suleiman Isa ya biya sadaki dubu 50 kuma yace yayi farin ciki matuka da ya auri masoyiyar sa Sanchez inda yace shekara daya da haduwan su Kenan sukayi aure kuma a bangaren sa banbancin shekaru ba wani abu bane.

Ita ma amarya Sanchez tayi farin ciki da auren masoyin nata kuma tace taji dadi da akayi auren ganin cewa ansha dagewa a baya sakamakon annobar COVID-19.

Amarya Sanchez dai bazawara ce a baya kuma ta haifi ya’ya biyu a Lindon in California kuma tace zata koma kasar amurka da angon nata bayan bikin

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Related stories

Leave a Reply