Uwargidan Gwamnan Jihar Borno Ta Bada Gudumuwar Kayan Abinci Da Kudade Ga Mata Da Suka Rasa Mazajen Su

images (19)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Uwargidan gwamnan jihar Borno Hajiya Falmata Babagana Zulum tayi rabiyar kayan abinci da kudade ga yan gudun hijira krista da wadanda suka rasa mazajensu 500 domin yin bikin kirsimeti.

Yayin da take mika kayayyakin, uwargida Falmata tace ta bada gudumuwar ne don basu damar kasancewa musamman ma a wannan lokaci na bikin kirsimeti wanda ya bukaci baiwa gajiyayyu da masoya.

Ta bukace su da suyi amfani da lokacin wajen yin addu’an zaman lafiya da cigaban jihar Borno, dama najeriya badaya inda tace babu wata al’umma da zata cigaba muddin babu tsaro.

Uwargidan gamnan ta kuma yi amfani da damar taja hankali jama’a das u kula a matakan kariya na musamman a wanna lokaci da ake fuskantar bazuwarta karo na biyu.

Datake jawabi, shugaban wadanda suka rasa mazajen nasu Asabe Dalagu, tace taimakon yazo musu a lokacin da ake bukata kuma ta bukaci masu kyawawan halaye da kungiyoyi da suyi koyi da kyautatawar uwargidan.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply