UN-OCHA ya ce rikici ya hana mutane 685,000 samun ilimi a yankin Arewa maso Gabas.

Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya (UN-OCHA) ya ce rikici ya hana mutane 685,000 samun ilimi a yankin Arewa maso Gabas.

Ofishin ya bayyana hakan yayin taron su na farko kan kidididigar ta shekarar 2021 wanda majalisar Dinkin Duniya ta fitar ranar Lahadi ga ‘yan jarida a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Mutanen da ake sa ran zasu samu ilimin na boko sun kai miliyan 1.1, amma 342,000 kawai aka samu duk da cewa ana bukatar dala miliyan 51.3 wato naira biliyan (N19.5) don ilimin yankin; amma kashi 1 kawai aka samu aka ɗauki rahotansu a wannan shekarar.

Binciken ya bayyana cewa kimanin yan gudun hijira 2,000 aka yi wa harkar Ilimi, wanda ya kunshi yara kanana tsakanin shekaru uku zuwa 17.

Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta kuma bayyana cewa sama da yara 340,000 ne suka samu ilimin a cikin garuruwan a jihohin Borno, Adamawa da Yobe bi da bi.

Adadin rikice-rikicen da ke faruwa a tsakanin yara maza da mata da ke samun ilimi ta hanyar cibiyoyin karatun ya kai ga dalibai 828 kawai, yayin da yara 576,897 suka yi niyyar a zangon farko na shekarar 2021. Don inganta hanyoyin koyarwa da ilmantarwa.

Ta kuma bayyana cewa membobin kwamitin gudanarwa na makarantu 204 ne aka horar daga cikin mambobin kwamitin 6,666 da aka yi niyya.