
Tsohon ministan wasanni na tarayya Mr Solomon Dalung ya bayyana cewa hakika jam’iyyar APC ta baiwa yan Najeriya kunya sabili da rashin cimma bukatun su.
Mr Dalung ya bayyana hakan ne yayin hira da gidan rediyon BBC muryar Hausa a safiyar yau.
Ya kuma ce duk da cewa shima dan jam’iyyar ne, yana da muhummanci ya furta gaskiya domin ya shafi yan Najeriya.
Kuma a game da batun rashin tsaro a yankin na Arewa maso gabas, Mr Dalung yace tabbas tafiye-tafiye a wannan lokuta ya zama damuwa sannan ya shawarci dukkan matafiya da suyi addu’a kafin shiga hanya.

