TETFund, Za Ta Dauki Nauyin Kafa Wasu Dakunan Binciken Kwayoyin

Babban Jami’in Asusun Ilimin Manyan Makarantu ya ce amincewar da aka bayar don tallafin bincike za a ninka shi a 2021 sama yadda aka amince a shekarar 2020.

Sakatare Janar na TETFund, Farfesa Suleiman Bogoro, ya ce za a sanar da amincewar da zaran kwamitin Amintattu ya tabbatar da hakan.

Farfesa Bogoro ya bayyana hakan ne a garin Abuja a ranar Talata, yayin da ya ke karbar wata tawaga ta National Institute for Policy and Strategic Studies, NIPS, Kuru, Babban Kwalejin Zartarwa na 43, 2021.

Ya bayyana cewa cibiyoyin da suka cancanta za su samu akalla N50 miliyan na tallafin bincike daga Naira biliyan 7.5 a Asusun Bincike na Kasa.

Shugaban na TETFund din ya ce a cikin kasafin kudin na 2021, wanda ke jiran amincewa, hukumar za ta dauki nauyin kafa wasu dakunan binciken kwayoyin bincike da jigilar kwayoyin halittu da maganin cututtukan, da kuma binciken allurar rigakafi da gano bakin zaren annobar COVID-19.

A cewarsa, a karkashin umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari, asusun ya samar da tsakanin N250 zuwa N300 don kafa, aƙalla, kashi ɗaya bisa huɗu na ɗakunan binciken kwayoyin cutar a Kasar.