Tawagar Sanatocin Najeriya Sun Kai Ziyara Jihar Borno

senatesmall
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Tawagar sanatocin wanda shugaban masu rinjaye Sanata Yahaya Abdullahi ya jagoranta sun kai ziyara birnin dake jihar Borno don yiwa gwamnan jihar Babagana Umara Zulum jaje kan mutuwar da mutane da dama sukayi sakamakon harin Boko Haram.

Tawagar sun hada da Senator Orji Uzor Kalu, Senator Yahaya Alh. Yawu, Senator Kashim Shettima, Senator Mohamed Ali Ndume da Senator Abubakar Kyari.

Yan tawagar sun samu tarba daga mataimakin gwamnan jihar Umar Usman Kadafur daga filin saukar jirage inda ya rakasu fadar gwamnatin jihar ska gana da gwamna Governor Zulum.

Yayin da yake jawabi a madadin majalisar Senator Yahaya ya tabbatar cewa bazasu gaji ba har sai an samu zaman lafiya mai dorewa a kasar baki daya.

Haka nan yace yan majalisar ne suka umarci shuaban majalisar yaje ya gana da shugaban kasa kan matsalar tsaron da ake fama da ita a kasar.

Senator Yahaya Abdullahi ya yabawa gwamnan Babagana Umara Zulum kan kokarin da yake na farfado da zaman lafiya a jihar Borno.
A nashi jawabin bayan ya yi musu barka da zuwa gwamnan ya yaba da goyon bayan da majalisar take bashi kan cigaban yankin na arewa maso gabas.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply