Tarayyar Turai Tabada Goyon Bayanta Ga Ayyukan Farfado Da Yankunan Da Rikici Ya Shafa A Kananan Hukumomi 3 Na Jihar Yobe

yobe mai mala
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gidauniyar matasan afirka na cigaba, zaman lafiya da karfafawa tare da tallafi daga tarayyar turai a jihar Yobesun gudanar da taro domin kawar da tashin hankali a jihar.

An gudanar da tarrukan ne a knanan hukumomin Gujba da Potiskum na jihar Damaturu domin karfafa kawunan jama’a musamman ma mata da yara a yankunan da abin ya shafa.

Shugaban kungiyar Abdullahi M Machina yace ayyukan zai samo maslaha ga matsalolin hadin kai wanda fitinan da aka fuskanta ya haifar tare da cewa aikin zai sa hankali kan sasantawa da kuma bada kulawa kan matsalan rudani ga mata da yara da sukayi alaka day an kungiyar Boko Haram a baya.

Jerry Ogiri yace mata da yara sune kashin bayan al’umma kuma a son hakane za’a mara musu baya
Wani mazaunin yankin Abdullahi Muhammad daga Dogonni a Potiskum yace hakika ayyukan motsa jiki yana janwo hadin kai a duniya musamman ma tsakankanin matasa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply