Sojojin Najeriya Sun Kashe Yan Kunar Bakin Wake 2 A Gamborun Ngala Dake Jihar Borno

female-bomber
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar operation lafiya dole dake aiki a karamar hukumar Gamborun Ngala dake jihar borno sun samu nasarar kasha wasu mata yan kunar bakin wake da sukayi yunkurin tada bama-bamai dake kunshe a jikinsu.

Wannan jawabin ya fito ne a wani sako da mataimakin diraktan hulda da jamaa na rundunar, kanal Onyema Nwachkuwu ya rattabawa hannu.

Sakon ya kara da cewa yan matan sunyi kokarin budewa a lokacin da akayi yunkurin dakatar dasu daga nesa.
Nwachukwu ya shawarci jamaa da su rika bayarda rahoton duk wani abinda bai kwanta musu a rai ba ga jami’an tsaro mafi kusa.

Mataimakin darakatan ya kuma gargadi jama’a dasu daina baiwa yan ta’addan mafaka. Wannan gargadin ya biyo bayan wani sako da daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin najeriya birgediya ganar Sani Usman ya fitar dangane da wannan zargin.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply