Sojojin Najeriya Sun Kama Mutum 2 Da Suke Kaiwa Yan Boko Haram Man Fetur

bh fuel distributors
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunan sojojin najeriya sun kama wasu mutum 2 da ake zargin suna kaiwa yan boko haram man fetur a garin Nafada dake jihar Gombe a Nigeria.

Mutanen 2 da ake zargi sune Mohammed Adamu Zika da Bukar Adamu Haji daya direban gidan mai ne dayan kuma mai kula da gidan mai ne a wani gidan mai dake jihar Gombe.

Rundunan sojojin ta fitar da rahoton ne ta bakin daraktan hulda da jama’a na rundunar Brigadier General Texas Chukwu inda yace suna nan suna bincike don su mika su gun wadanda suka dace.

A baya dai an gargadi gidajen man dake yankin Nafada dasu daina siyar da man da ya wuce ka’ida ga masu motoci. Haka nan an kirayi jama’a dasu kai rahoton duk wanda basu yadda dashi ba ga jami’an tsaro mafi kusa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply