Sojojin da sukaji Raunika Yayin Fafatawa Da Yan Boko Haram Sun Koka Kan Cewa Baa Basu Hakkokinsu.

nigerian-army-troops-1024x576-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Sojojin da suka jikkata yayin da suke yaki da yan taaddan Boko Haram a jihar Borno, Arewa maso Gabas kasar sun koka kan cewa anyi watsi dasu kuma ba a biyansu alawus dinsu.
Da yake zantawa da manema labarai a asibitin sojoji da ke Kaduna, sojojin sunyi korafin cewa ban da albashinsu, har yanzu ba a biyasu hakkokin su yanda ya kamata .
Wasu daga cikin sojojin , sun baiyana cewa anfi bawa marasa lafiyar fararan hula kulawa ta musamman a Asibitin Sojoji dake Kaduna, fiye da su sojojin da suka jikkata a filin daga .
Jami’in Hulda da Jamaa na Runduna ta 1, da ke Kaduna, Kanar Ezundu Idimah ya yi watsi da zargin, inda yace zance bashi da wata makama belle Toshe
Wani jamiin sojan da ya samu zaunika a Fagan daga, harma ya rasa wani sashi na jikin sa ya ce bai samu wani diyyar nakasa ba, amma an biyasa albashin sa cikin gaggawa.
Wani soja, da ya ji rauni a watanni uku da suka gabata bayan kwanaki kadan da yin bikin aurensa, yace ya kasance cikin raɗaɗin ciwo tun lokacin da abin ya faru, kuma ya kasa yin aikin
Ya kara da cewa Bayan faruwar lamarin, an dauki tsawon watanni ana kulawa da shi a Maiduguri kafin daga baya a tura shi zuwa Asibitin Sojojin dake , Kaduna, inda aka yi masa jinyar na tsawon watanni hudu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply