
Rundunar sojojin Najeriya tayi nasarar dakile wani harin yan kungiyar Boko Haram a karamar hukumar Mafa na jihar Borno.
A cewar wani jami’in sa kai na CJTF wanda ya gani da idon sa yace yan ta’addan sun shigo da misalign karfe 6 da minti 20 na yamma kusa da kauyen Kasasewa a karamar hukumar Mafa.
Ya kara dacewa sun shigo da motocin yaki akalla 8 dauke da bindigogi da Babura suna ta harbe harbe, yayin da jami’an tsaro suka fara yakar su wanda hakan ya sanya su ka gudu tare da barin makaman su.

Yace an kashe yan ta’addan wanda bai san adadin suba.
Har yanzu dai jami’an sojoji da sauran jami’an tsaro basu ce komai ba game da harin.
