Sojoji Da ‘Yan Sanda Sun Samu Sabani Gamai Da Kubutar Da Daliban Islamiya Da Aka Sace A Jihar Katsina

troop3
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hedikwatar tsaro ta ce sojojin Operation Hadarin Daji tare da hadin gwiwar ‘yan sanda da’ yan sintiri na yankin a ranar Asabar sun ceto dalibai 39 daga hannan ‘yan ta’adda a karamar hukumar Dandume da ke jihar Katsina.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, Gambo Isah, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, yace jami’an’ yan sanda da ‘yan banga sun kubutar da dalibai 80 na Hizburrahim Islamiyya da aka sace da shanu 12 daga’ yan ta’adda a daren Asabar.

mai Magana da yawun rundunar tsaro, Manjo Janar John Enenche ya ce sojojin sun samu kiran ne da misalin karfe 11:30 na daren ranar Asabar daga kauyen Mahuta cewa wasu ‘yan bindiga suna tafiya tare da wasu yara’, islamiyan da shanayan sata.

inda daga nan ne sojojin suka hallara zuwa wurin, inda su kayi kwanton bauna tare da toshe hanyar ’yan fashi a kan hanyar Daudawa-Kadisau da Sheme Mairuwa da ƙauyen Unguwar Audu.

Bayan haka, sojoji sun binciki yankin tare da kubutar da ‘yan matan 39 da aka sace da kuma shanaye takwas.

Wadanda aka sachin a hanzu haka an hada su da danginsu yayin da shanun da aka kwato aka ba wa masu ita .

babban kwamandan sojojin ya yaba wa Dakarun sojojin da sauran jami’an tsaro kan nasarorin da suka samu.

Ya kuma yaba wa mazauna yankin da ’yan banga game da hadin kan da suke bayarwa wajen magance matsalolin tsaro a jihar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply