Sojin Najeriya Sun Kashe Yan Bindiga 80 Da Kama 33 A Arewa Maso Yammacin Kasar

Nigerian_Nigeria_army_soldiers_military_combat_field_uniforms_007
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar sojin Najeriya ta samu kyakyawar nasara a kokarin yaki da take da ‘yan bindiga, masu satar shanu, masu garkuwa da mutane da wasu muggan laifuka a yankin arewa maso yamma inda suka ce sun kashe yan bindiga 80 da kama 33 a yankin.

Jami’an yankin karkashin Operation Sahel Sanity sun ceto wadanda akayi garkuwa dasu su 17 hade da kama masu basu rahoto 14 da kuma masu hadin baki dasu a jihohin Sokoto, Katsina da Zamfara.

Yayin da yake ganawa da manema labarai daga sansanin Super Camp na 4 dake Faskari a jihar Katsina mataimakin daraktan tsaron ta fannin yada labarai Brig.-Gen. Benard Onyeuko inda yace rundunar baza ta gajiya ba har sai ta kakkabe su daga yankin baki daya.

Haka nan yace an kafa Operation Hadarin Daji don kula da ayyukan yan bindiga, masu satar shanu, masu garkuwa da mutane da sauran muggan laifuka.

San nan yace jami’an sun lalata sansanin yan bindigar mai suna Dangote Triangle da makansu da kuma wasu sansanonin nasu.

Haka nan yace sun samu shanu 943, raguna 633. Sai kuma makamai da suka hada da bindigar AK-47 7, bindiga mai inji 1 da kuma bindiga kirar hannu 16.

Ya kuma kara da cewa shugaban rundunar Lt.-Gen. Tukur Buratai ya yabawa jami’an saboda kwarewar su kan ayyukan da suke gudanarwa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply