Shugabn Yansandan Najeriya Yace Faifan Bidiyon Da wani Jami’in Tsaro Ke cin zarafin Wani Ba A Kasar Bane

igp
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

An ja hankalin rundunar yansandan Najeriya kan wani faifan bidiyo da ake yadawa na yadda wani jami’in tsaro ke cin zarafain wani wanda hakan ya saba dokar yancin dan adam da mutuncin shi da yancin shi.

A faifan bidiyon an ga jami’in tsaron na taka wuyan mutumin da kafarsa inda har mutumin ya kasa motsi a kasa.
Rundunar tayi alla wadai da abun inda tace ta duba kuma ta tantance cewa abun ba a najeriya ya faru ba.

Kuma idan akayi duban tsanaki za’a ga abubuwan hawan dake fitowa a bayansu ba irin wadanda ake amfani dasu a Najeriya bane, san nan idan aka duba lambobin ma za’a ga akwai banbanci dana najeriya. Haka nan jami’in tsaron da aka gani yasa kaya irin na ma’aikatan tsaro na kamfanoni masu zaman kansu wanda za’a iya samu a ko ina.

San nan sunce dansandan bana Najeriya bane, haka ma yaren dake fita cikin bidiyon ba yaran Najeriya bane.

Shugaban yansandan najeriya M.A Adamu yayi kira ga jama’a dasu yi watsi da wannan faifan bidiyon wanda kawai yana nuna son ayiwa jami’an tsaron kasar nan kazafi san nan yayi ya tabbatar wa jama’a cewa suna mutun ta yan kasa da kuma basu damarsu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply