shugabannin kasar Sun Bukaci Da Ayiwa Wadanda Zasuje Kallon Wasan Da Masu Buga Wasan Allurer Rigakafin Covid-19.

sakamakon kwallon kafa na duniya da kasar Qatar ta shirya na shekarar 2022, shugabannin kasar sun bukaci da ayiwa wadanda zasuje kallon wasan da masu mara musus baya allurer rigakafin Covid-19.

ministan kasashen wajen kasar ta Qatar Mohammed Bin Abdulrahman Al-Thanine ya bayyana wannan muhimmin bayanin inda yace kasar na fatan yiwa duk wanda zai halarci bikin wasan rigakafin.

inda yace hakan zai sa a samu raguwa na yaduwar cutar ta Covid-19, bayan da kasar ta sake samun bullar cutar harda rasuwar mutane.

Minister Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani yace suna nan suna tattaunawa da masu samar da rigakafin ganin yadda duk masu halarta zasu samu.

ya kuma bayyana cewa akwai yiwuwar abubuwa zasu kamala kafin ana I gobe za’a fara wasan.