Shugaban ‘Yansandan Najeriya Ya Bukaci Kwamishinoninsa Dasu Karbo Makaman Dake Hannun Mutane

POLICE-IG-ADAMU
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban yansanda Mohammed Adamu ya bukaci kwamishinonin ‘yansanda na jihohi 36 a fadin kasar ciki harda Abuja dasu nemo duk makaman dake hannun mutane ba bisa ka’ida ba kuma su kama masu su, san nan su mika su ayi musu hukunci.

Adamu ya bayyana a rahoton da mai Magana da yawun rundunar Frank Mba yasa hannu cewa ya bada umarnin ne ganin yadda ake bawa mutane makamai musamman ‘yan bangar siyasa da wasu masu aikata ayyukan ta’addanci a fadin kasar.

Haka nan ya bada umarninbayan da ake shirin gudanar da zaben gwamnonin jihohin Edo da Ondo.

Mba a rahotonsa yace an bada umarnin ne kamar yadda yake a cikin kundin tsarin mulkin kasar na mallakar makamai.

Haka nan yace ya kamata kwamishinonin suyi taron wayar da kai ga hukumomin tsaron dake fadin jihohin kasar don tabbatar da bin dokoki.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply