Shugaban ‘Yan Tawayen Sudan Ta Kudu Machar Yaki Sa Hannu Kan Yarjejeniyar Tsagaita Wuta

Sudan rebel chief Riek Machar
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban ‘yan tawayen Sudan ta kudu Mista Riek Machar, ya ki sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakinsu da gwamnati domin ganin an kawo ‘karshen rikicin da ke aukuwa a sassan ‘kasar Sudan.

Ministan harkokin wajen ‘kasar Sudan Al-Dierdiry Ahmed ya shaidawa manema labarai cewa ‘yan tawayen SPLM 6angaren Machar sun ki cimma yarjejeniyar da aka shata domin samar da zaman lafiya a sassan ‘kasar Sudan baki daya.

Wasu jam’iyyu a yankin Sudan ta kudu sune suka ware wannan makon da nufin zama teburin sulhu a birnin Khartoum domin kawo ‘karshen rikicin da ya lakume rayukan dimbin al’umma da kuma sanya gommai zama ‘yan gudun hijira tun daga watan Disamban shekarar 2013.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply