
Abdulrazaq MUNGADI, Gombe
Mukaddashin yansandan Najeriya Mohammed Adamu yayi kira ga mazauna jihar Gombe da sauran jihohin kasar dasu hada karfi wajen yaki da ta’addanci a kasar.
Wakilin Dandal Kura Radio International daga jihar Gombe Abdurazak Auwal Mungadi ya rawaito cewa mukaddashin shugaban kasar yace za’a samu tsaro ne idan jama’a suka hada kai da jami’an tsaro.

Mr Adamu ya bayyana haka a taron bude kwamitin yansandan farin kaya wanda gwamnatin jihar ta Gombe ta kafa. Mataimakin mukaddashin na shiyya ta 3 Halliru Abubakar Gwandu ne ya wakilci shugaban inda yace rundunar yansandan shekaru da dama tana kokarin ganin ta gudanar da ayyukan da suka dace.
Haka nan yace rundunar na kokarin kafawa da samar da sashin dakile muggan laifuka a jihar e explained da kuma yankin da zai kula da dakile muggan ayyukan matasa cikin al’umma.
A nashi bangaren gwamnan jihar Muhammadu Inuwa Yahaya bayyyana cewa gwamnatinsa zata cigab da tabbatarda an samu hadin kai da jami’an tsaro a jihar don samun zaman lafiya mai dorewa cikin al’umma
