Shugaban majalisar dattijai ya dora laifin rikicin jihar Oyo akan shugabannin yankin

ahmed lawan
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban majalisar dattijai Dr. Ahmad Ibrahim Lawan ya mika laifin rikicin yankin na kudu maso yamma akan shugabannin yankin inda yace sune suka tunzura mutanensu suka farwa yan Arewa dake yankin suna kasuwanci.

Bayanain na Lawan ya biyo bayan rikicin da aka samu akasuwar Sasha a jihar Oyo satin day a gabata wanda yayi sanadiyyar rasuwar mutane da dama da asarar dukiyoyinsu da miliyoyin Nairori.

Ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa da gidan radiyo BBC sashin Hausa wanda wakilinmu ya hada mana rahoton daga Maiduguri inda yace Lawan bawa shugabannin yankin kudu maso yamma laifin kisan mutanen a garin na Ibadan.

Acewarsa yadda shugabanci ya lalace a yankin ne yasa wadan nan rikicin suke faruwa a jihar ta Oyo da sauran abubuwan dake faruwa a yankin.

Haka nan ya jaddada cewa wasu gwamnonin na iingiza jama’arsu ta hanyar daukar makamai suna farwa yan arewa mazauna yankunansu ta hanyar maganganu dake sa bata gari su kasha yan arewa.

Gidan radiyo Dandal Kura Radio ya rawaito cewa kwanakin baya an samu rikici tsakanin Yarabawa da Hausa a kasuwar Shasa dake karamar hukumar Akinyele a Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Inda aka samu mutane da dama da suka raunana a sansanin Hausawa da Yarabawa yan kasuwa inda hausawa kimanin 5,000 da mata da yara suka rasa matsugunansu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply