Shugaban Kasar Najeriya Ya Kirayi Matasan Kasar Dasu Jira Zuwa Shekarar 2023

President-Miuhammadu-Buhari-wide-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasar Najeriya muhammadu Buhari yasa hannu kan bawa matasa damar tsayawa zabe amma ya kirayi matasan dasu jira zuwa shekarar 2023.

Yasa hannu a gaban matasan da aka zaba daga jihohi 36 a fadin kasar da babban birnin tarayya. Buharin ya bayyana cewa an rage shekarun yan majalisar jiha da majalisar kasa daga 30 zuwa shekara 25, shugaban kasa kuma daga 40 zuwa shekara 35.

Haka nan ya bayyana damuwarsa kan dalilin da yasa ba’a rage na sanatoci da gwamnoni ba kamar yadda aka bukata inda yace yakamata a duba wan nan lamarin. Ya kara da cewa matasa na matukar bada gudunmawa a damokaradiyyar kasar da kuma siyasa.

Samson Itodo, wanda yayi Magana a madadin matasan ya yabawa shugaban kasar inda yace shugaban ya kafa tarihi, kuma ya bayyana takaicin sa da yadda jihohin Zamfara, Legas da Kano suka ki yadda da dokar a majalisun su na jiha.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply