Shugaban Kasar Najeriya Ya Halarci Bikin Ranar Sojoji A Jihar Borno

Buhari
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasar najeriya Muhammadu Buhari ya halarci bikin ranar sojoji na shekarar 2018 a karamar hukumar Mongunu dake jihar Borno a Najeriya ranar Juma’a, inda ya tabbatar da zakulo masu hura wutar rikici da hukunta su a wasu jihohi da ake gudanar da rikici.

A rahoton da babban mataimakin shugaban kasar ta fannin yada labarai Malam Garba Shehu yace Buharin ya bayyana hakan yayin rufe taron ranar sojojin na shekarar 2018.

Ya kara da cewa shugaban ya maimaita abinda ya fadawa shugabannin kiristoci ranar Alhamis yayin jawabi rikicin manoma da makiyaya.
Yayinda yake godewa jami’an sojin kan kokarin tsare kasar, ya tabbatar da har yanzu akwai wasu matsalolin. Haka nan ya tabbatarwa duniya da yan Najeriya cewa gwamnatinsa na nan na kokarin yadda za’a saki ragowar yan matan chibok da daya data rage a cikin yan matan Dapchi wato Leah Sharebu.

Haka nan Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya bayyana cewa harin kunar bakin wake alama ce ta rashin karfi.
Ministan tsaro Brigadier-General Mansur Dan Ali ya yabawa jami’an sojin da suka kafa jami’ai masu aiki da Baburan hawa don karfafa tsaro a guraren da motoci basa iya shiga. Haka nan ya godewa jami’an sojin sama kan samar da masu bada agajin gaggwa a bangarori 6 a kasar.

Haka nan shugaban tsaron kasar General Gabriel Olonisakin ya kara da cewa ayyukan da sojojin suke gudanarwa a Arewa maso gabshin kasar ya karkata kan taimakawa fararen hula da rikicin ta’addanci ya shafa don su koma garuruwansu.

Shugaban sojojin Najeriya General Tukur Buratai yace an zabi Monguno don gudanar da bikin na shekarar 2018 don a nuna nasarar da aka samu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply