
Shugaban kasar najeriya Muhammadu Buhari ya jagoranci taron tunawa da manyan jaruman kasar dasuka kwan da dama tareda masu ruwa da tsaki.
Mataimakin shugaban kasar yemi osibanjo, shugaban majallisar dattijai ahmad lawan, shugaban majjallisar wakilai femi gbajabiamila da shugaban alkalai tanko Muhammadu ne suka jagoranci shugaban tsaron kasar dan tunawa da mazan jiya da suka kwan da dama a babban birnin abuja najeriya.
Babban mai bawa shugaban kasar shawara kan al’amuran labarai, femi Adesina, ranar al’ahamis ya bayyana takarda mai dauke da taken security checklist, a matsayin alama ta tunawa da manyan jaruman dasuka kwan da dama.

Adesina ya kara da cewa , shirin ya bude sabbabin hanyoyi na nasara da ma’aikatun tsaron sukeyi wajen magance rashin tsaro a kasar.
