Shugaban kasar Mali da Friminista Sunyi Murabus.

Shugaban kasar Mali da friminista sunyi murabus bayan kokarin da ake na daidaita kasar kamar yadda kasashen duniya suka tabbatar.

Baba Cisse babban mai bada shawara na musamman ga Assimi Giota yace shugaba Bah Ndaw da friminista Moctar Ouane sunyi murabus bayan juyin mulkin da ya maida mulkin farin hula a watan August da ta gabata, a yanzu dai ana tattaunawa game da sakin su da kuma daura sabon gwamnati.