Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Taya Dr. Daniel Ismaila Shaga, Murna Zama Hama Bachama.

buhari
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Dr. Daniel Ismaila Shaga, murna zama Hama Bachama.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu.

Shugaban ya kuma jinjinawa sarakunan masarautar Bachama da gwamnatin jihar Adamawa bisa zaben Dr Shaga, a matsayin sarkin duba da irin gogewar sa da cancanta sa.

Shugaba Buhari yace bayan ritayar Dakta Shaga a matsayin Mataimakin Kwamandan Janar na Miyagun Kwayoyi daga Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi ta Kasa a 1994, ya sadaukar da lokacinsa da a matsayin kwararren, mai ba da shawara kan haraji.

Shugaban kasar ya shawarci Dakta Shagas da ya himmatu wajen nuna kwazo, da ya kamata da kuma rikon amana ga mutanen yankinsa dama ‘yan Najeriya.
Shugaba Buhari yayi masa fatan samun nasara da kariyar Allah.

PRR/MGS/RGK/BBW BBW HDG/SFI/BBW

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply