Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Mika Ta’aziyar Sa Ga Gwamnatin Jihar Borno

buhari1
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyar sa ga gwamnatin jihar Borno da jama’an jihar bisa rasuwar Sarkin Dikwa, Shehu Muhammad Abba Masta.

Mataimakain shugaban kasa kan harkokin yada labarai Garba shehu shi ya fitar da hakan cikin sanarwa.

Cikin sakon ta’aziyar shugaban kasar ga Shehu Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, davgwamnatin da kuma jama’an jihar baki daya, shugaban kasar yace marigayin basaraken ya rasu a daidai lokaci da najeriya take bukatar sa.

Ya kuma kwantatan sarkin a matsayin mutum na gari wanda yayi aiki domin al’umman sa wanda kuma najeriya gaba daya zata rasa irin ayyukan sa.

Shugaban kasa yayi addu’an Allah ya gafarta masa kuma Ya saka masa da Aljanna sannan Ya baiwa iyalan sa juriyan rashi.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply