Shugaban kasa Muhammad Buhari Yace Gwamnatinsa Ta Shirya Yaki Da Cin Hanci da Ta’addanci A Sakon Sabuwar Shekara 2021

president-muhammadu-buhari
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammad Buhari yace Gwamnatinsa ta Shirya yaki da Cin Hanci da Ta’addanci a Sakon Sabuwar Shekara 2021

A Cikin Bayaninsa na Sabuwar Shekara ga Al-ummar Najeriya Shugaban Kasa Muhammad Buhari yayi Bayanin Magance wasu Matsaloli a Cikin Wannan Shekarar ta 2021 inda yace za’a Kawo Tsarin Garan Bawul a Aikin ‘Yan Sanda, ya kuma Bayyana Cewar yana sane da matasan Kasar wajen Tallafa musu Domin Cigaban Rayuwarsu.

ya kara da Cewar Matasan Najeriya Mutane ne masu Hazaka da Kwarewar Ayyuka a Fadin Duniya baki da inda yace Gwamnatinsa a Shirye take domin bunkasa matasa.

Shugaban Kasa Buhari yace Gwamnatinsa zatayi yaki da Cin hanci da Rashawa tare da Ta’addanci a Najeriya, ya Kuma Bayyana Irin Hazaka ta Jami’an Tsaro Wajen Kwato Daliban Makarantar Kankara ta Jihar Katsina.

Haka Zalika Shugaban kasar yayi Magana akan Irin hare haren da Kungiyar Mayakan Boko Haram Suke yi a Kasar inda yace yana iya bakin kokarinsa, ya kuma ce Mutane sutuna yadda Kasar take a Bayan Kafin zuwansa duba da Yadda Wasu Lamura suka Gyaru zuwa Yanzu.

Yayi Alkhawari ga ‘Yan Najeriya Wajen Bijiro da Ayyukan Cigaba tare da Cika Al kawarin daya Dauka Kafin Darewa a Karagar Mulki.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply