Shugaban Fasa Kauri Reshen Jihar Borno Ya Yabawa Gidan Radiyon Dandalkura

COMTROLER NIS BORNO COMMAND Ismail Muhammed Hamis LETF, FARUQ DALHATU MD DKRI RIGHT
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By: Babagana Bukar Wakil, Maiduguri

Shugaban jami’an fasa kauri reshen jihar Borno Ismail Muhammed Hamis yace manema labarai na bada gudunmawa ta musamman wajen yada sahihan labaran da suka dace a kasar nan.

Shugaban ya bayyana hakan yayin da jami’an kafar sadarwa mai zaman kanta ta farko a jihar Borno wato Dandalkura suka kai masa ziyara wanda Manajan darakta Alhaji Faruq Dalhatu ya jagoranta a hedikwatarsu dake Babbar sakariya.

Yayin da yake jawabi kan ziyarar tasu Manajan Daraktan na gidan Radio Dandal Kura Alhaji Faruq Dalhatu yace a farko an kafa gidan Radiyon a shekarar said 2015 wanda UAID ta kafa don samar da labarai kan yan kungiyar Boko Haram a Arewa maso gabas da kuma yankin Tafkin Chadi.

Alhaji Faruq ya kara da cewa Dandal Kura Radio International tayi aiki karkashin tallafi na shekara biyu a yankin wanda daga baya aka tsaida shi amma suka cigaba da aikin don bawa mutane sakonni da rahotanni da mutanen yankin suke bukata.

Haka nan Alhaji Dalhatu ya bayyana cewa gidan radiyon na Dandal Kura na gabatar da shirye-shirye a matsakaicin zango na SW wanda ake ji a duniya baki daya cikin harsunan Kanuri da Hausa.

San nan ya kara da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya basu lasisin gudanar da ayyukan zango na FM wanda ake ji a fadin jihar Bornobaki daya.

A nashi jawabin shugaban fasa kaurin na jihar Borno Ismail Muhammed Hamis ya yabawa ayyukan gidan radiyon Dandal Kura ta dakile rikici ta hanayar wayar da kan jama’a cikin harsunan Kanuri and Hausa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply