Shugaban Buhari Yace Gwamnatin Na Kokarin Fitar Da Mutane Kimanin Miliyan 100 Daga Kangin Talauci .

buhari-talkingwidth-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci hukumar kula da masu bukata ta musamman dasu taka muhimmiyar rawa ganin yadda gwamnatin take kokarin fitar da mutane kimanin miliyan 100 daga kangin talauci a kasar.

Shugaban kasar ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da sababbain shugabannin hukumar ta masu bukata ta musamman a fadar shugaban kasar dake Abuja.

Yace ya kamata suyi aikin da zai taimaka wajen cimma burin gwamnatin nasa na fitar da mutane miliyan 100 daga talauci a kasar ta Najeriya.

Haka nan yace gwamnatin zata kaddamar da wasu ayyuka wadanda zasu amfani masu bukata ta musamman da kuma cigaban su.
San nan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa zata cigaba da saka masu bukata ta musamman cikin ayyukanta.

Haka nan shugaban yayi alkawarin cewa gwamnatinsa zata cigaba da alaka da yankunan duniya na yankuna daban daban don habbaka rayuwar jama’ar kasar.

San nan ya godewa wasu gwamnoni wadanda suka saka dokoki kan masu bukata ta musamman inda ya bukaci ragowar da suma su yi abinda ya dace.

A nashi bangaren Dr Hussaini Kangiwa shugaban hukumar ta masu buktata ta musamman ya bayyanawa manema labarai cewa sunje fadar shugaban kasar don godiya ga shugaban kasar kan taimakon da yake bawa masu bukata ta musamman a kasar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply